Taron kasa: APC ta ce a kai kasuwa

Image caption Jiga-jigan jam'iyyar APC a Najeriya, Janar Buhari da Bola Tinubu

Jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya ta ce ba za ta shiga cikin taron kasa da gwamnatin Tarayya ke shirin yi ba.

APC bayan taron 'yan kwamitinta na zartarwarta a Abuja, ta ce akwai lauje a cikin nadi a yinkurin Shugaba Jonathan na shirin taron tattaunawa na hada kan kasa.

Kakakin jam'iyyar APC, Alhaji Lai Muhammed wanda ya yiwa manema labarai jawabin bayan taron, ya ce abinda Shugaba Jonathan ke shirin yi, za a iya yinsa a lokacin yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima.

A cewar APC, tunda Shugaba Jonathan ya ce duk abinda kwamitin taron kasa ya tattara, sai majalisar dokokin ta yi mahawara a kai, ya kamata a bar maganar taron domin majalisa tayi aikinta.

Alhaji Lai Muhammed, ya ce shirin yin taron kasa da gwamnati ke son a yi wata dabara ce ta kawar da alkibilar kasa daga manyan matsalolin da suka addabi jama'a.

Karin bayani