Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 37

Image caption Sojoji na sintiri a titunan Maiduguri

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe mayakan Boko Haram su 37 a luguden wuta ta sama da kasa a kan sansanin 'yan kungiyar a jihar Borno.

Kakakin rundunar soji a shiya ta bakwai, Kyaftdin Aliyu Ibrahim Danja ya ce sun lalata wasu sansanonin 'yan Boko Haram sannan suka kashe wasu a musayar wuta.

Rundunar sojin ta kaddamar da harin ne a sansanin dake Alagarno dake jihar Borno.

A cewar kakakin, sun kwato makamai da alburusai daga wajen 'yan kungiyar.

A ranar Lahadin data wuce, mayaka 'yan Boko Haram suka kashe matafiya su 19 kusada kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Tun lokacin da aka soma bata kashi tsakanin 'yan Boko Haram da jami'an tsaron Najeriya, rahotanni sun ce an kashe mutane fiye da 3,600.

Karin bayani