EFCC ta musanta hannu a cin hanci

Image caption EFCC ta ce rahoton yunkuri ne kawai na shafa mata kashin-kaji

Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta musanta sakamakon wani rahoto da ke cewar hukumar na cikin jerin hukumomin da ke karbar cin hanci da rashawa a Nigeria.

Hukumar dai ta ce rahoton wani yunkuri na a shafa mata kashin-kaji a yakin da take yi da masu aikata cin hanci da rashawa a kasar.

Ta kara da cewa tana yin tababa a kan matakin da aka bi wajen tattara bayanan sakamakon binciken.

A farkon makon nan ne dai gidauniyar neman tabbatar da adalci ta CLEEN da hadin gwuiwar Cibiyar MacArthur Foundation suka fitar da wani rahoto da ke cewar rundunar 'yan sanda da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na kasar, watau ICPC da EFCC na daga cikin hukumomin gwamnatin da cin hanci da rashawa ke tasiri a aikace aikacensu.

Karin bayani