Shugabannin EU za su gudanar da taro

Wasu shugabannin kasashen turai
Image caption Wasu shugabannin kasashen turai

Shugabannin kasashen turai za su gudanar da wani taro a yau alhamis a dai dai lokacin da ake ci gaba da nuna bacin rai game da zargin cewa hukumar leken asirin Amurka na nadar bayanan wayar tarho jama'a a nahiyar turai.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande na matsin lamba na ganin an tattauna batun, bayan samun rahotan cewa ana nadar bayanan wayar salular miliyoyin 'yan kasar Faransa.

A jiya ne dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kira shugaba Obama ta wayar tarho bayan samun bayanan cewa mai yiwuwa hukumar leken asirin Amurka na nadar bayanan wayar salular ta.

Kakakin gwamnatin Jamus Steffen Sheibert ya ce Mrs Merkel ta bukaci a yi mata cikakken bayani game da zargin nadar bayanan wayar salular ta da ta bayyana da cewa cin amana ne.

Sai dai kakakin fadar White House Jay Carney ya shaida wa manema labaru cewa Mr Obama ya tabbatarwa Mrs Merkel cewa Amurka ba ta nadar bayanan wayar salular ta.

Ya kara da cewa shugabannin kasashen biyu sun amince da su kara karfafa hukumomin leken asiri kasashen su da zummar inganta harkokin tsaro tare kuma da kare hakkokin 'yan kasar su.