Gwamnati za ta binciki Stella Oduah

Ministar sufurin jiragen sama ta Najeriya, Stella Oduah
Image caption Wata kungiya mai ikirarin yaki da cin hanci a Najeriya ta nemi ministar ta yi murabus

Gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti na mutum uku, domin biniken ministar zirga-zirgan jiragen sama, Stella Oduah game da zargin sayen motocin alfarma.

An baiwa kwamitin wanda tsohon shugaban ma'aikata na kasa Bello Sali ke jagoranta, makonni biyu ya kammala aikinsa.

Ministar dai bata halarci taron ministoci da aka yi a Abuja ba, ko da yake fadar shugaban kasar bata bayyana dalilin rashin halartarta ba.

Tun da fari dai fadar shugaban kasar ta nemi Ms. Stella Oduah ta yi bayani game da badakalar motocin.

Ana zargin Ministar ce da tilasta wa daya daga cikin hukumomin da ke karkashin ma'aikatarta, ta saya mata motocin guda biyu a kan kudi fiye da naira miliyan 250.