An yi wa buduwar dashen fuska a China

Image caption Likita a wani asibiti a kasar China

An yi wa wata budurwa 'yar shekaru 17 dashen fuska a China, inda aka yi amfani da fatar da aka dasa a kirjinta.

Likitoci sun redo tsokar cinyar Xu Jianmei sannan aka dasa tsokar a kafadarta ta hagu kafin ayi tiyatar.

Daga nan kuma sai aka saka wata karamar jakar ruwa a karkashin tsokar don fatar ta kara girma, daga bisani aka ciro fatar aka saka fuskarta.

Yarinyar da aka yi wa dashen sabuwar fatar, ta gamu da matsalar kuna ce sakamakon gobara lokacin tana da shekaru biyar da haihuwa lamarin da ya lalata mata fuskar.

A kwanakin baya, an yi wa wani mutum dashe hanci a goshinsa a kasar ta China.