Yau ECOWAS za ta fara taro a Dakar

Image caption ECOWAS za ta duba yiwuwur samar da kudi bai daya

A yau Juma'a ne shugabannin kasashen Afrika ta Yamma ke fara wani taro a Dakar babban birnin kasar Senegal karkashin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen ta Ecowas.

Taron da zai hada shugabannin kasashen goma sha biyar zai mayar hankali ne kan wasu batutuwa guda uku da suka hada da siyasa da tsaro da tatalin arziki.

Taron shine karo na farko tun bayan da Kasar Mali ta gudanar da zaben shugaban kasa.

Sai dai kasar Guinea Bissau da makwabciyarta Guinea na fama da rikicin siyasa.

Wani batu kuma da taron zai mayar da hakali akai ya hada da cire kudaden shigowa da kaya ga 'yan kasuwar kasashen da bude kofofin cinikayya tsakanin su da Tarayyar Turai.

Haka kumaza a tattauna batun samar da takardar kudi bai-daya.

Karin bayani