Kamfanin Areva zai dakatar da aiki a Nijar

Wani kamfanin Areva a Nijar
Image caption Wani kamfanin Areva a Nijar

A jamhuriyar Nijar kamfanin Areva mai hakar uranium ya ce mai yiwuwa daya daga cikin kamfanoninsa da ke yi masa ayyukan, Somair, ya dakatar da ayyukansa a karshen wannan watan.

Kamfanin na Areva ya dora laifin dakatar da ayyukan kamfanin a kan hukumomin Nijar da ke son sake duba yarjejeniyar da ke tsakaninsu da kamfanin na Areva.

Zargin da wani babban jami'in kamfanin kula da albarkatun ma'adanan kasar, SOPAMIN ya karyata, yana mai cewa ba haka zancen yake ba.