Motoci: Stella Oduah ta maida martani

Image caption Minista Stella Oduah

Ministar Zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya ta rubuta wasika ga shugaban kasa Goodluck Jonathan inda tayi bayanin abin ta sani dangane da sayen motocin masu sulke da ake zargin ta yi ba bisa ka'ida ba.

Fadar shugaban kasar dai ta sanar da cewa ta kafa wani kwamiti na mutum uku wanda zai binciki zarge-zargen da ake yi, sannan majalisar wakilai ta kasar ma ta ce za ta gudanar da bincike a kan lamarin.

Ana zargin Stella Oduah ce da tursasa daya daga cikin hukumomin da ke karkashin ma'aikatarta ta saya mata motoci guda biyu a kan kudi naira miliyan 225.

Itama majalisar dokokin kasar ta umurci kwamitinti mai kula da zirga-zirgar jiragen sama ta bincike yadda aka sayi motocin a kan wannan kudin mai yawa.

Karin bayani