Sabon zargin badakalar miliyan 600 kan Stella Oduah

Image caption 'Yan majalisar sun zargi Stella Oduah da hannu kan cinikin motoci ba bisa ka'ida ba.

A Najeriya, zargin da ake yi wa ma'aikatar sufurin jiragen saman kasar ya kara girma.

Hakan dai ya faru ne sakamakon ikirarin da wani kwamitin Majalisar Wakilan kasar ya ce ya bankado wani cinikin motoci da ma'aikatar ta yi ba bisa ka'ida ba, wanda ya kai sama da naira miliyan 600.

A ranar Alhamis ne dai kwamitin ya sanar da haka bayan ya fara jin bahasi daga bangarorin da abin ya shafa.

An dai kafa kwamitin ne don ya binciki cinikin da ma'aikatar ta yi na sayen motoci biyu masu sulke a kan kudi naira 255.

Kwamitin dai, kamar yadda 'yan majalisar suka ce, ya gayyaci dukkan wadanda maganar ta shafa, ciki har da ministar sufurin jiragen sama, Stella Oduah, da jami'an hukumar da ke kula da harkokin jiragen sama da na hukumar da ke kula da harkokin cinikin gwamnatin tarayya da kuma kamfanin Koscharis Motors.

Sai dai kuma ministar ba ta halarci zaman ba saboda an ce ta yi bulaguro zuwa kasar Isra'ila tare da shugaba Goodluck Jonathan.

Karin bayani