Mata 100 muryar rabin al'umma

A cikin shekaru biyar a jere, kasar Iceland ta kasance kasar da tafi kowacce rage yawan gibi tsakanin maza da mata, kamar yadda kungiyar tattalin arziki ta duniya-WEF ta bayyana.

Bayanan sun nuna cewar kasar Iceland kasa ce da mata ke samun daidaito da maza a bangaren ilimi da lafiya sannan kuma suna shiga harkar siyasa ana damawa dasu. Kasashen dake kan jerin sune; Finland, Norway da kuma Sweden a cikin rahoton da aka fitar a shekara ta 2013. Gaba daya, an samu raguwa wajen nuna bambamci tsakanin maza da mata a duniya a shekara ta 2013, inda aka yi nazari kan kasashe 86 cikin 136 wato 93 cikin 100 na al'ummar duniya, kamar yadda Saadia Zahidi ta bayyana. An duba bangaren lafiya da ilimi, da aikin yi da siyasa kamar yadda muka saka a taswirar dake kasa.

Yaya aka tantance kasashen?

Don kwatanta tazarar dake tsakanin jinsi, kungiyar WEF ta kirkiri wani ma'auni daga bayanan da ake samu fiye da 10. Maki 1 (ko 100%) na nuna babu bambamci; 0 (ko 0%) na nuna akwai bambamci. An baiwa kasashe matsayi bisa alkaluman da aka samu.