Dokar hana fita ta sa'o'i 24 a Yobe

Image caption Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Geidam

An kafa dokar hana fita ta sa'o'i 24 a jihar Yobe, bayan da aka shafe sa'oi da dama a daren jiya ana musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram a Damaturu.

Rahotanni sun ce mazauna Damaturu babban birnin jihar sun kwana cikin zullumi sakamakon jin karar harbe-harbe da aka shafe sa'o'i ana yi babu kakkautawa a daren ranar Alhamis.

Kawo yanzu babu cikakken bayanai game da irin hasarar rayuka da dukiyoyi da aka yi sakamakon tashin hankalin.

Karin bayani