Jamus na nuna fushi kan leken asirinta

Image caption Amurka na fuskantar fushin Jamus kan leken asiri

Kasashen Faransa da Jamus sun yi kira da a kulla yarjejeniya da Amurka daga nan zuwa karshen wannan shekarar a kokarin warware takaddamar da ake yi game da leken asirin da Amurkar ke yi.

Hakan dai ya biyo bayan bayanai ne dake nuna cewar mai yiwuwa hukumomin leken asiri na Amurkar suna sauraren zantuka na wayoyin tarho na Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel da wasu miliyoyin layukan waya na Faransa.

Angela Merkel yayin da take magana a ranar farkon taron Kungiyar taryyar Turai a Brussels ta nanata cewa aminci ga Hukumar leken asirin Amurka ya gurgunta bisa rahotanni da ke cewa ana sauraron zantukan wayoyin da take yi na tafi da gidanka.

Merkel ta kara da cewa duk da babu shaidu kwarara kan bibiyar da ake mata amma akwai kwararan alamu sannan kuma tun da Shugaba Obama bai musanta ba ya sa Jamus ta yadda cewa anyi sauraron zantukan ta.

Karin bayani