'Zargin leken asiri na lalata dangantaka'

Image caption Amurka na ganin zargin leken asiri na shafar dangantaka

Amurka ta amsa cewar zargin baya-bayan nan da ya nuna cewar tana yi wa aminanta leken asiri ya haddasa rashin jituwa tare da gurgunta dangartakarta da gwamnatocin kasashen Turai.

Jen Psaki, wata mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce bayanan da suka hada da sauraren layin wayar Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun sa mutane sun shiga 'yar tsama da Amurka.

Tace kuskure ne a bari wadannan bayanai su dagula kokarin da ake yi na warware batutuwan da suka shafi kasashen Syria da Iran.

Tace, gwamnatin Obama tana duba yiwuwar aiki da shawarwarin da kasashen Jamus da Faransa suka gabatar na tsaurara dokokin da suka shafi harkokinta na neman bayanan sirri.

Karin bayani