A Najeriya kwamitin taron kasa ya isa Calabar

Image caption Najeriya na shirin taron kasa

A Najeriya, kwamitin da shugaban kasa ya kafa don shirya babban taron kasa ya isa garin Calabar babban birnin Cross River.

Kwamitin dai yana sauraron ra'ayoyi da shawarwarin jama'a kan yadda za a shirya taron da kuma abubuwan da za a tattauna.

Wasu jama'ar yankin kudu maso kudancin kasar na cewa idan za a tattauna batun raba Najeriya a wajen taron to kada ma aba su goron gayyata; domin ba sa goyon bayan a raba kasa.

Taron dai da ake shirin yi ya sami suka daga wasu sassa na kasar da ma wasu jihohi cewa ba za su halarta ba saboda zargin abinda za a kudun duno a taron don cimma wata manufa.

Karin bayani