Mata a Saudiya sun bijirewa dokar tuka Mota

Mace ta na tuki
Image caption Mace ta na tuki

Mata a Saudiyya sun kaddamar da tuka mota da kansu inda suka bijire wa dokar da ta haramta mu su tuka motoci.

Kungiyoyin farar hula masu rajin kare hakkin dan Adam sun shafe tsawon makonni su na Kampe domin jawo hankali.

Tun da farko Minista mai kula da al'amuran cikin gida na Saudiyya ya gargadi matan su guji karya dokar hana mata tuki wadda aka kafa tun shekarar 1990.

Mutane goma sha bakwai ne su ka sanya hannu akan wata takardar koke dake neman a dage haramcin da aka sanyawa direbobi mata, amma 'yan tsirarun hutunan bidiyo ne aka sanya akan shafukan sada zumunta na intanet wanda ke nuna mata a sassa daban-daban na biranen Saudi Arabia su na tuka motocin su.

Babu mace daya da dan sanda ya tsayar duk da yake hukumomi sun yi gargadi akan cewa ka da matan su kuskura su karya dokar.

Masu fafutukan da akayi imanin cewa su na shirye-shiryen shiga cikin zanga-zangar, ma'aikatar cikin gidan kasar ta tuntube su kai tsaye kuma ta basu shawarar kada su yi hakan.

Wannan shi ne karo na uku da matan Saudia ke gudanar da zanga-zanga akan haramcin da aka sanya musu wanda kuma aka tilasta musu bi fiye da shekaru ashirin da suka gabata.

Hala Al-Dosari marubuciya ce kuma mai fafutuka mazauniyar birnin Jedda ta shaidawa BBC cewa, munyi imanin cewa wadannan masu fafutuka da su ke goya mana baya, za ayi musu bita da kulli tun daga sama.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba