Saudiyya ta yi gargadi kan zanga-zanga

Image caption An gargadi mata kada su yi zanga-zanga a Saudiyya

Hukumomi a kasar Saudiyya sun kara jaddada gargadin da suka yi ga Mata kada su keta haramcin da aka yi wa matan masu tuka motoci ta hanyar shiga wata zanga-zangar gama gari.

Matan dai sun shirya yin zanga-zangar gama-gari a yau Asabar don nuna rashin amincewa da dokar hana su su yi tuki.

Ma'aikatar cikin gida ta kasar ta sake jaddada cewa duk wanda ya karya dokar - zai iya fuskantar hukuncin da ba a bayyana shi ba.

Wannan zanga-zangar ita ce ta irinta ta uku da aka shirya tun a shekarar 1990.

Wakiliyar BBC ta ce, tukin, daya ne kawai daga cikin bukatun Matan da daama, shi yasa gwamnatin ba ta son bayar da kai bori ya hau.

Karin bayani