An kashe mutane arba'in a harin bam a Syria

An kai harin bam a Syria
Image caption Mutanen da aka raunata a harin bam na Syria

Wani bam da aka dana a Mota wanda ya tarwatse a wani Masallaci kusa da Damascus babban birnin Syria ya hallaka wasu mutane tare da raunata wasu mutanen masu yawa.

Gwamnati da 'yan adawa suna nuna ma juna dan manuni a kan alhakin kai harin a Suq Wadi Barada.

Kamfanin dillancin labaran Syria ya ce bam din ya tarwatse ne a lokacinda 'yan tawaye ke kokarin dana shi.

Amma kungiyar 'yan adawa ta National Coalition ta zargi sojojin Shugaba Assad da laifin dana bama-baman a cikin motoci biyu a kusa da masallacin.

Kungiyar dake sa ido ga al'amurran keta hakkin dan adam a Syria ta ce mutane a kalla 40 ne aka kashe a wannan hari.