Gwamnatin Bangladesh na fuskantar bore

Image caption Gwamnatin Bangladesh na dada fuskantar bore

Gwamnatin Bangladesh na fuskantar karin wani boren na siyasa yayin da aka shiga rana ta uku ta yajin aikin gama gari da ake yi a kasar.

Jam'iyyar adawa ta BNP dake karkashin jagorancin Khaleda Zia ta yi kiran da a dakatar da duk wasu harkoki na kasar don matsa lamba a kan gwamnati ta ba da damar kafa gwamnatin wucin-gadi wadda za ta sa ido ga zaben da za a yi cikin watan Janairu.

Za a cigaba da yajin aikin ne duk da rokon da Prime Minister Sheikh Hasina ta yi wa Mrs Zia ta wayar tarho na neman a dakatar da yajin aikin.

Ana ganin wannan shine karon farko da abokan hamayyar suka yi magana da juna kai-tsaye cikin kimanin shekaru goma.

Karin bayani