Sojoji a Congo sun kwato garin Kibumba

Image caption Sojoji a Congo sun fatattaki 'yan tawaye a Kibumba

Sojoji a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo sun ce sun sake kwato ikon mulkin garin Kibumba dake gabashin kasar bayan fatattakar 'yan tawaye na kungiyar M23.

Wani kakakin sojan ya ce 'yan tawayen sun arce sun nufi yankin dake kan iyakar kasar da Rwanda.

Ranar Jumm'a ne aka gwabza fadan a kusa da birnin Goma kwanaki da dama bayan rushewar tattaunawar zaman lafiya da aka yi a Kampala babban birnin Uganda.

Koene Vervake wakili na musamman na kungiyar Tarayyar Turai a yankin ya shaidawa BBC cewar yana cikin matukar damuwa.

Yace, "tattaunawar da aka yi a kwanan baya ta yi zafi kwarai, to amma ba a kai ga cimma cikakkiyar yarjejeniya ba.

Wannan dai shine fada mafi muni da aka gwabza a gabashin kasar ta Congo cikin kimanin watanni biyu.

Karin bayani