Nijar na neman mai gina dam din Kandaji

Dam
Image caption Dam

Gwamnatin Nijar tana shirye shiryen daukar wani sabon kamfanin da zai maye gurbin kamfanin ZVS na kasar Rasha wajen ginin dam din Kandaji.

Gwamnatin ta Nijar dai ta kwace wa kamfanin na ZVS kwangilar ayyukan ne, saboda a cewarta ya kasa.

Wani bincike da hukumomin na Nijar suka sa aka yi ya gano cewa, kamfanin na ZVS zai ranka wa Nijar biliyan 10 na CFA daga cikin kudaden da ya karba ba tare da ya yi ayyukan ba yadda ya kamata.

Shugaban hukumar da ke kula da ayyukan ginin dam din na Kandaji, Malam Amadu Haruna ne ya bayyana hakan a cikin hirar da yayi da BBC.

Ana fatan sabon kamfanin da za a mika wa aikin ginin dam din zai fara aikin ne a watan Fabrairun 2014, ya kuma kammala shi a shekara ta 2016.

Ana kyautata zaton dam din na Kandaji zai sa a sami bunkasar ayyukan gona a Nijar din, da isashiyar wutar lantarkin da ma za a iya sayar wa kasashen waje.

Masu tallafa wa kasar wajen ginin dam din za su yi taro a mako mai zuwa a Yamai domin tattaunawa a kan batun.