Kungiyoyi na damuwa kan fyade a Najeriya

Image caption Mata na fuskantar barazanar fyade

A Najeriya kungiyoyi masu zaman kansu na ci gaba da nuna damuwa bisa yawaitar fyade a kasar.

A wani taro da wata kungiya mai suna Peace Revival and Reconciliation Foundation ta gudanar a Kaduna ta yi kira ga limaman addinin musulunci da na addinin kirista da su rika wa'azi kan fyaden.

Kungiyar tana muradin malaman addinan su ware wasu lokuta kamar Jumma'a da Lahadi lokuttan da jama'a ke taruwa; don kara fadakar da jama'a game da illolin dake tattare da fyade.

Bugu da kari, Kungiyar ta nuna bukata ga gwamnati ta tsaurara hukuncin fyade; ganin har kananan yara ke fadawa cikin wannan matsalar a yanzu.

Karin bayani