Syria ta cika wa'adin makamai masu guba

Sufetocin Majalisar Dinkin Duniya
Image caption Sufetocin Majalisar Dinkin Duniya

Kungiyar OPCW mai fafutukar hana amfani da makamai masu guba ta ce gwamnatin Syria ta mika shirye-shiryenta na lalata makaman da ta jibge.

A cewar kungiyar, a ranar Alhamis ce Syriar ta mika takardun, kwanaki uku kamin cikar wa'adin da aka bata.

Nan da karshen yinin yau OPCW na fatan ziyartar dukan wurare ashirin da uku inda Syriar ke kera makaman masu guba ko kuma take ajiye su.

Ya zuwa ranar Juma'ar da ta wuce kungiyar ta OPCW ta samu ta ziyarci wurare goma sha tara.

Kuma nan da ranar daya ga watan Nuwamba mai zuwa ne ya kamata ta lalata makaman.

Kasashen duniya sun tashi tsaye wajen daukar mataki a kan Syriar ne, bayan da aka yi amfani da makaman masu guba a kan fararen hular da basu ji ba basu gani ba.