An hallaka wasu kusoshin al shabaab

Mayakan al Shabaab
Image caption Mayakan al Shabaab

Jami'ai a Somalia sun ce an kashe wasu kusoshin kungiyar 'yan gwagwarmayar Islama ta al-Shabaab a Somalia, a wani hari da ake kyautata zaton hari ne da aka kai da jirage marasa matuka.

Ana jin cewa daya daga cikinsu kwararre ne wajen tsara yadda za a kai hare-haren kunar bakin wake.

Wasu mazauna yankin sun shaidawa BBC cewa wani makami mai linzami ne ya fada kan wata mota a kusa da garin Jilib, yayin da take hanyar zuwa Mogadishu.

An ce sun taso ne daga garin Barawe mai tashar jiragen ruwa, wanda matattara ce ta al-Shabaab.

Dakarun musamman na Amurka sun kai samame garin na Barawe a farkon watan nan, a wani yunkuri na kama wani jagoran kungiyar ta Al-Shabaab da ake dangantawa da harin da aka kai a cibiyar kasuwanci ta Westgate a kasar Kenya.