Cutar Amai da gudawa na yaduwa a Najeriya

Image caption Cutar Amai da gudawa na kisa a Najeriya

Yanzu haka dai cutar amai da gudawa na cigaba da yaduwa a jihohi dabam-dabam na arewacin Najeriya tare da haddasa hasarar rayuka.

Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin kasar ta kasance ta baya-bayan nan da aka samu barkewar cutar.

Rahotanni na cewa akalla mutane biyu sun rasa rayukan su, yayin da wasu kuma ke karbar magunguna a asibiti sakamakon barkewar cutar a yankin karamar hukumar Jibiya.

Tuni dai cutar ta haddasa asarar rayuka a Jihohin Filato da Sakwato da Kuma Zamfara mai makwabtaka da Jihar ta Katsina.

Karin bayani