Ana zargin Kamfanin Birtaniya da sakaci

Image caption Ana zargin Kamfanin Birtaniya da gallazawa fursunoni

An zargi wani kamfanin tsaro na Birtaniya G4S da laifin tafka ayyukan assha da sakaci da aiki a gidan Yarin da ya fi kowanne hadari a Afrika ta kudu.

An ba da rahoton cewa an rinka yin allurai da karfin tsiya da sawa wasu daga cikin fursunoni dubu uku wayoyin lantarki don hukunta su a gidan Yaarin dake Mangung na kusa da Blom-fontein.

Lauyansu ya yi Allah wa dai da al'adar halin ko in kula ta jami'an gidan yarin ke yi.

Sai dai kuma kamfanin tsaron na G4S na Birtaniyar ya ce shi, bai ga wata shaida ba ta zargin aikata laifi da ake zargin ma'aikatan na sa ba, ya kuma dora laifi a kan rikicin da ake samu a gidan yarin a kan jayayya ta kwadago.

Karin bayani