Ruwa da iska na barazana a Ingila

Image caption Birtaniya na fuskantar barazanar ruwa da iska

A Birtaniya, wani ruwa da iska mai karfi da masu hasashen yanayi suka ce zai iya zama daya daga cikin iska mafi muni da ya shafi kasar cikin shekaru da dama ya keta kudanci da tsakiyar Ingila.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake shekawa ya riga ya shafi wasu daga cikin yankunan.

Haka kuma akwai iska mai karfi dake tafiyar sama da kilomita dari da talatin cikin sa'a guda dake ratsawa a yankin.

Cibiyar kula da yanayi ta kasa ta yi kashedin cewa ruwan da iska mai karfi za su iya kada itace da lalata gine-gine tare da haddasa ambaliyar ruwa.

An gargadi mutane su guji yin tafiye-tafiye; an ma kai ga soke tashin jiragen sama 60 da kuma tsayar da jiragen kasa da dama daga aiki.

Karin bayani