Cutar Malaria ta hallaka mutane a Kamaru

Image caption Rashin tsabtace muhalli kan janyo malaria

Rahotanni daga arewacin kasar Kamaru na cewa cutar zazzabin cizon sauro ta kunno kai a Lardin arewa mai nisa inda lamarin ya tsananta a birnin Marwa.

Alkalumma sun nuna sama da mutane dubu arba'in da biyu ne suka kamu da cutar, a yayinda kuma kusan dubu daya ne ake kiyasta cewa sun rasa rayukansu.

Wadanda suka fi kamuwa da cutar sune yara da kuma matasa masu shekaru daga goma sha biyar zuwa kasa.

Masana na ganin cewa tsanantar da cutar ta yi na da alaka ne da rashin yin amfani da gidan sauro da kuma rashin tsabtace muhalli.

Zazzabin cizon sauro na hallaka dubban mutane a duniya musamman a nahiyar Afrika.

Karin bayani