Mutane na nuna damuwa kan cutar cholera

Image caption Ma'abota shafinmu na Facebook sun yi kira ga jama'a da hukumomi su dauki matakan kawar da cutar.

Ma'abota shafin sada zumunta na BBC Hausa Facebook, sun bayyana matukar damuwarsu game da cutar amai da gudawa da ke addabar wasu jihohin arewacin Nigeria.

Sun bayyana ra'ayoyinsu ne a shafin namu, suna masu yin kira ga jama'a da su dauki matakan kula da kiwon lafiya wajen kare kansu daga kamuwa daga cutar.

Kazalika, sun yi kira ga hukumomi su samar da tsaftataccen ruwan sha da kuma wasu matakai na tabbatar da tsaftar muhalli.

A ra'ayinsa, Babah Nwachukwu, ya ce ''ya kamata jama'a su dinga tsabtace muhallinsu don kaucewa wannan annoba ta amai da gudawa''.

Shi kuma Muhd Yusuf, kira ya yi ga gwamnatoci daban-daban da su dauki mataki, yana mai cewa '' gwamnatin Nijeria da sauran hukumomi na cikin gida da waje ku dada ba da dauki da gudunmawa ga wadanda cutar amai da gudawa ta shafa. Sauran mutane kuma Allah ya kare''.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa cutar ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a jihohi irinsu Sokoto da Filato da Yobe da Jigawa da kuma Katsina.

Karin bayani