Ana caccakar Amurka game da leken asiri

Image caption Hukumar tsaro Amurka wato NSA na fuskantar kalubale daga kasashen duniya.

An gayyaci jakadan Amurka a kasar Spain ya gana da ministocin gwamnati a birnin Madrid, domin bada bayanai kan zargin cewa hukumar tattara bayanan Sirri ta Amurka na musu leken asiri.

Kafafen yada labarai a Spain na cewa a cikin wata daya kacal, a boye an rika sa ido kan maganganun waya har guda miliyan sittin a Spain.

Daga cikin bayanan da aka samu daga tsohon jami'in leken asirin Amurka, Edward Snowden, cikin watan Disamban bara ne aka rika sa ido kan inda aka yi wayoyin da kuma tsawon lokacin da aka dauka ana wayar.

Wata tawaga daga majalisar dokokin tarayyar Turai za ta gana da manyan jami'an tsaron Amurka, da wasu 'yan majalisar dokoki a birnin Washington, domin tattara bayanai, bisa zargin da aka yi na baya bayan nan cewa Amurka na satar sauraren maganganun shugabannin Turai, da ma na al'umarta.

Ita ma shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel za ta tura wasu jami'an ayyukan sirri zuwa Washington domin neman bayani kan zargin cewa an shafe shekaru goma ana satar sauraren wayoyinta.

Karin bayani