Karzai zai gana da Sharif a Birtaniya

Hamid Karzai
Image caption Hamid Karzai

Shugaban Afghanistan Hamid Karzai ya fara ziyarar kwanaki biyar a Birtaniya domin tattaunawa da shugaban gwamnatin Pakistan Nawaz Sharif.

Kasar Birtaniya ce za ta jagoranci tattaunawar da pirai minista David Cameron ya shirya a ziyarar da ya kai Kabul, da nufin kyautata alaka tsakanin kasashen biyu.

Haka kuma gwamnatin Birtaniya za ta bukaci tabbacin zaman lafiya a Afghanistan daga wajen shugaba Karzai, gabannin zabubbukan da za'a gabatar a kasar cikin watan Aprilu.