Badakalar "Jihadin Jima'i" a Tunisia

mayakan Tunisia
Image caption mayakan Tunisia

Al'ummar Tunisia na cigaba da kace-nace game da batun "jihadin jima'i" da ake zargin wasu mata a kasar na aikatawa.

Labarin dai ya samo tushe ne daga yankin tsaunukan Chambi da ke kan iyakar Tunisia da Algeria, inda tun cikin watan Disamban 2012 ake dauki-ba-dadi tsakanin sojin Tunisia da mayaka masu alaka da al-Qaeda.

Mahukuntan Tunisia sun ce sun kama 'yan mata a yankin da su ke zargi da aikata jima'i da mayakan domin karfafa musu gwiwa.

Farfagandar Siyasa

Sai dai al'ummar kasar na tababar wannan batu yayinda iyalan 'yan matan su ka shiga halin dimuwa.

Badakalar "jihadin jima'i" ta kara tasowa ne bayanda ministan harkokin cikin gida Lotfi bin Jido yace mata na zuwa cikin tsaunukan kasar da kuma Syria domin tallafawa mayaka ta hanyar jima'i.

Ya shaidawa majalisar dokokin kasar cewa "Yan tawaye kimanin 20 zuwa 100 ne kan sadu da 'yan matan Tunisia da sunan "jihadin jima'i" yayinda mu ke nan ba ma yin komai akai."

Sai dai wasu manazarta na kallon wannan zargi a matsayin farfagandar siyasa mara tushe.

Ba Musulunci ba ne

Wani fitaccen malamin Musulunci a Tunisia Sheikh Fareed Elbaji ya shaidawa BBC cewa ya san iyalan da 'ya'yansu mata su ka je Syria domin ba da tallafin jima'i ga mayaka, bayanda suka samu fatawa daga wasu malamai a Syria.

Yace; "Masu bada fatawar na fakewa ne da cewa larura na halatta abinda ya haramta - inda su ke halatta auren mutu'ah ko kuma aure mai kayadadden wa'adi domin biyan bukatar 'yan tawayen."

Sai dai ya ce; "Musulunci ya haramta auren mutu'ah domin daidai ya ke da karuwanci."