Burtaniya na karbar bakuncin taron Kasashen Musulmi

Firai Ministan Burtaniya
Image caption Za a tattauna batun zuba jari da ayyukan yi

A yau ne ake soma taron Kasashen Musulmi na duniya kan tattalin arziki a birnin London.

Wakilai sama da dubu daya da dari biyar ne ake sa ran za su halarci taron, wanda shi ne taron tattalin arziki mafi girma ga kasashen musulmi kuma wannan ne karon farko da ake yin sa ba a kasar da ke da rinjayen musulmi ba.

Mahalartan dai za su hada da shugabannin gwamnatoci da na manyan kamfanonin kasashen musulmi ciki har da Alhaji Aliko Dangote dan Najeriya da ya fi kowa arziki a Afrika.

Babban jami'in hulda da jama'a na bankin raya kasashen Musulmai, IDB Dr. Muhammed Jameel Yusha'u, na daga cikin wadanda za su halarci taron kuma ya fadawa BBC cewa za a tattauna batutuwan da suka shafi zuba jari da samawa matasa ayyukan yi.