Leƙen Asiri: Amurka ta kare kanta

Gwamnatin Amurka ta kare shirinta na tattara bayanan sirri a Turai.

Sai dai ta amsa cewa lallai watakila sai ta sauya salon da take amfani da shi.

Kakakin fadar White House, Jay Carney, ya ce tattara bayanan sirrin ya taimaka wa Amurkar wajen kare Amurkawa da abokan kawancenta.

Ya ce, irin wannan alaƙa na da muhimmanci wajen tabbatar da tsaro a Amurka, da ma a ƙasashe ƙawayenta.

Ya ce lallai bayanan da suka taso na baya bayan nan, sun haddasa cece-kucen diplomasiyya.

Kuma yayin da ake da sabbin hanyoyin fasaha na zamani, mai yiwuwa akwai buƙatar sa wasu karin sharudda kan yadda ake tattara bayanai.