Birtaniya za ta ware hannayen jari na Halal

Kasuwar hannun jari ta London
Image caption Kasuwar hannun jari ta London

Pirai ministan Birtaniya, David Cameron zai kaddamar da jerin hannayen jari na halal a kasuwar hada-hadar hannun jari ta London, a wani bangare na taron tattalin arzikin Islama na duniya.

Ana kuma sa ran Pirai ministan zai sanar da cewa Birtaniya za ta zamo kasar da ba ta Musulmi ba ta farko da zata nemi rance ta hannun al'umma bisa tsarin Shari''a.

Za'a iya kaddamar da takardar rancen, da ake kira sukuk da larabci, da ta kai dalar Amurka miliyan 300 a farkon shekarar badi.

Taron tattalin arziki na Musulunci da ake farawa yau a London, shi ne karo na farko da ake gudanarwa a kasar da ba ta Musulmi ba.