Birtaniya za ta zama cibiyar hannayen jarin Halal

Image caption David Cameron

Pirai Ministan Birtaniya David Cameron ya bada sanarwar wasu sababbin shirye-shirye na harkokin hada-hadar kudade da suka dace da shari'ar Musulunci.

A jawabinsa ga wani babban taro a kan harkokin kudi bisa tsarin Musulunci da ake yi a London, Mr Cameron ya bayyana cewar kasuwar hada-hadar hannayen jari ta London, za ta kaddamar da wani sabon hannun jari na shari'a sannan kuma baitul malin Birtaniya za ta bayar da takardun basussuka bisa tsarin Islama.

Dama dai birnin London tuni ya zama wata cibiya ta gudanar da hada-hadar kasuwanci bisa tsarin addinin Islama.

A bisa irin wannan tsari akan bayar da jari ne ba wai bashi ba, wanda idan aka samu riba akan wannan jari za'a biya ribar, ko kuma a biya kudin haya amma ba kudin ruwa ba.

Kasuwar hada-hadar hannayen jari ta London za ta kaddamar da wani sabon hannun jari wanda yayi daidai da tanadin shari'ar musulunci, domin baiwa musulmai masu sha'awar zuba jari damar yanke shawarar inda zasu zuba kudadensu.

Karin bayani