An saki Faransawa 4 da aka sace a Nijar

Image caption Shugaban Hollande da Shugaba Issoufou

An sako Faransawa hudu wadanda 'yan kungiyar Alka'ida reshen arewacin Afrika suka yi garkuwa dasu na tsawon shekaru uku a Jamhuriyar Nijar.

Shugaban Faransa, Francois Hollande shine ya bayyana haka a lokacin ziyarar da yake yi a kasar Slovakia.

Mr Hollande ya nuna godiyarsa ga Shugaba Muhammadou Issoufou wanda ya taimaka aka kubutar da mutanen.

An yi awon gaba da mutanen ne a watan Satumbar 2010 a wajen kwanansu dake garin Arlit inda suka aiki da kamfanin Areva mai ayyukan ma'adanin Uranium a Nijar.

A cewar Hollande, ministan harkokin wajen Faransa dana tsaro za su tafi Nijar don taho da mutanen nan bada jimawa ba.

Karin bayani