An kama sojojin da suka ci ganima a Kenya

sojojin Kenya a Westgate
Image caption sojojin Kenya a Westgate

An kori sojojin Kenya guda biyu tare da daure su a kurkuku bayanda aka same su da laifin kwasar ganima a harin da aka kai rukunin kantunan Westgate watan jiya.

Shugaban rundunar sojin Julius Karangi ya shaidawa manema labarai cewa akwai wani sojan na uku da yanzu haka ake bincikarsa.

Da fari dai yace sojojin ba su dauki komai ba sai ruwan sha a tsawon kwanaki hudun da harin ya dauka duk da hotunan bidiyo da suka nuna sojin na kwasar ganima a cikin kantunan da ke Nairobi.

Kungiyar al-Shabab ta Somalia ta ce ita ce ta kai harin da ya hallaka mutane 67.