An daure mai shirin kashe Mandela shekaru 35

Nelson Mandela
Image caption Nelson Mandela

An zartar da hukuncin daurin shekaru 35 a gidan yari kan jagoran turawa masu kin jinin bakar fata a Afrika ta kudu bayanda ya yi yunkurin kashe Nelson Mandela tare da hambarar da gwamnatinsa.

An yankewa Mike du Toit na kungiyar Boeremag hukuncin ne tare da mabiyansa 19 bayanda aka kwashe shekaru 10 ana sauraron shari'arsu.

A shekarar 2002 ne kungiyar ta shirya makarkashiyar juyin mulkin, sannan kuma ta dasa bama-bamai a Soweto, daura da Johannesburg.

Mr. Du Toit shi ne dan Afrika ta kudu na farko da aka samu da laifin cin amanar kasa tun bayan kare mulkin tsirarun turawa masu wariyar launin fata a 1994.