Mu'azu ya musanta ficewa daga sabuwar PDP

Muazu Babangida Aliyu
Image caption Muazu Babangida Aliyu

Gwamnan jihar Niger da ke arewacin Nigeria, Mua'zu Babangida Aliyu ya musanta zargin cewa ya balle daga tafiyar gwamnonin nan bakwai da suka kafa sabuwar PDP.

A baya bayan nan dai Mu'azu Babangida Aliyu bai halarci wasu tarurruka da aka yi na kungiyar gwamnonin bakwai ba.

Kakakin gwamnan Malam Danladi Muhammad Ndayebo ya shaidawa BBC cewa wannan batu ne da bashi da tushe balle makama.

Gwamnonin bakwai dai na nuna rashin amincewa ne da shugabancin Bamanga Tukur na jam'iyyar PDP, inda su ka ce suna shirin fita daga jam'iyyar domin kafa ta su ko kuma shiga wata.