Jonathan na son gabatar da kasafin kudin 2014

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya na neman iznin majalisar akan kasafin kudi

Shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan ya nemi izinin majalisar dokokin kasar don gabatar da kasafin kudin kasar na badi a ranar goma sha biyu ga watan Nuwamba na wannan shekarar.

Shugaban Kasar ya bayyana aniyarsa ne a cikin wata wasikar da ya aika wa majalisar dattawa da ta wakilan kasar.

Sai dai wannan wasika ba ta yi armashi ga wasu 'yan majalisar ba, sakamakon zargin da suke yi cewa babu wani abin kirki da bangaren zartarwar ya tabuka wajen aiwatar da kasafin kudin wannan shekarar, ballantana a shiga maganar kasafin kudin shekara mai zuwa.

A Najeriya 'yan adawa sun jima suna zargin cewa ba a aiwatar da kasafin kudi a duk shekara kamar yadda ya kamata.

Karin bayani