Admiral Mike Akhigbe ya rasu

Image caption Margayi Admiral Mike Akhigbe

Iyalan tsohon mataimakin shugaban gwamnatin Nigeria ta mulkin soji Admiral Mike Akhigbe mai murabus sun tabbatar da mutuwarsa sakamakon cutar daji.

Margayi Akhigbe ya kasance mataimakin gwamnatin mulkin soji a lokacin Janar AbdusSalami Abubakar.

Marigayi Mike Akhigbe wanda ya rike mukamai daban-daban a zamanin gwamnatocin sojin kasar na baya ya rasu ne sakamakon cutar dajin da ya yi fama da ita a makogwaronsa.

Shugaban Nigeria, Dr Goodluck Ebele Jonathan, ya mika ta'aziyarsa a madadin gwamnati da jama'ar Nigeria ga iyalai da 'yan uwa da kuma abokan arziki na tsohon mataimakin shugaban gwamnatin mulkin soji.