Yaki da cutar Shan Inna a Nijar

Rigakafin cutar shan inna
Image caption A bana ba a samu bullar cutar ba a Nijar

Hukumomin kiwon Lafiya a Jamhuriyar Nijar sun soma wani sabon zagayen diga wa yara ruwan maganin riga kafin cutar shan inna ko polio.

Aikin na gudana ne duk kuwa da cewa ba a samu rahoton yaro ko daya da ya kamu da cutar a kasar ba a wannan shekarar.

A wannan karon hukumomin kiwon lafiyan na ba da karfi wajen yiwa yara da al'umomin da ke kan iyaka da Najeriya rigakafin, bayan da aka gano mutane sama da arba'in da cutar a makwabciyar ta Najeriya a wannan shekara.

Ana sa ran aikin ya shafi miliyoyin yara daga haihuwa har zuwa shekaru 5, a cikin fafutukar da suke yi na kawar da cutar kwata kwata daga doron kasa.

Karin bayani