Cutar Polio ta barke a Syria

Image caption Wani yaro a Syria

Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ce an samu yara goma da suka kamu da cutar shan inna ko polio a arewacin kasar Syria.

Wannan shi ne karon farko cikin shekaru goma sha hudu da aka samu barkewar cutar shan innar a kasar ta Syria.

Hukumar ta WHO ta ce akwai yuwuwar cutar ta watsu cikin gaggawa a Syrair da kuma sauran kasashen yankin.

Ana dai kyautata zaton mayaka 'yan kasashen waje ne suka yada cutar a Syria.

Cutar Polio ta kasance annoba a kasashe uku a duniya wato Pakistan, Afghanistan da kuma Najeriya.

Karin bayani