Yaya Toure na yaki da farautar giwaye

Yaya Toure
Image caption Yaya Toure

Tauraron kwallon kafa Yaya Toure ya yi gargadin cewa kashe giwaye domin cinikin haurensu na barazana ga dorewarsu a duniya.

Toure, dan wasan Manchester City da Ivory Coast na magana ne a Nairobi babban birnin Kenya inda aka nada shi jakadan wayar da al'umma game da ayyukan shirin majalisar dinkin duniya game da kula da muhalli.

Yaya Toure yace giwaye 800 ne kacal suka rage a Ivory Coast duk da taken da ake yi wa kungiyar kwallon kafa ta kasar na 'The Elephants'.

A baya bayan nan dai an samun karuwar haramtacciyar farautar giwaye a Africa bayanda bukatar hauren ta karu a nahiyar Asia.