Za'a yiwa leken asirin Amurka garambawul

Dianne Feinstein
Image caption Dianne Feinstein

Shugabar kwamitin leken asiri na majalisar dattawa ta Amurka ta bukaci gudanar da gagarumin garambawul kan yadda kasar ke aikin leken asiri.

Diane Feinstein tace sauraron bayanan shugabannin kasashen da ke kawance da Amurka - ciki har da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel - ba daidai ba ne, kuma rashin sanar da shugaba Obama abubuwan da ke faruwa kuskure ne.

Tace fadar White House ta shaida mata cewa za'a dakatar da sauraron bayanan shugabannin sai dai wani babban jami'in gwamnatin ya shaidawa BBC ceaw kodayake an yi sauye-sauyen tsarin aiki, dokar ba ta sauya ba.

Da yammacin Talata ne dai shugabannin hukumomin leken asirin Amurka zasu gurfana gaban majalisar wakilan kasar domin amsa tambayoyi a gaban kwamitin majalisar kan leken asiri.