Yaya Toure na yaki da farautar giwaye

Yaya Toure
Image caption Yaya Toure

Tauraron kwallon kafa Yaya Toure ya yi gargadin cewa kashe giwaye domin cinikin haurensu na barazana ga dorewarsu a duniya.

Toure, dan wasan Manchester City da Ivory Coast, na magana ne a Nairobi babban birnin Kenya inda aka nada shi jakadan wayar da kan al'umma game da ayyukan shirin majalisar dinkin duniya game da kula da muhalli.

Yaya Toure ya ce giwaye 800 ne kacal suka rage a Ivory Coast duk da taken da ake yi wa kungiyar kwallon kafa ta kasar na 'The Elephants'.

A baya bayan nan dai an samu karuwar haramtacciyar farautar giwaye a Africa bayan da bukatar hauren ta karu a nahiyar Asia.

Abin yabawa

Image caption An yabawa Toure game da daukar wannan mataki

Shugaban hukumar da ke kare muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya, Achim Steiner, ya yi marhabin da matakin da Toure -- zakaran dan kwallon Africa kuma dan wasan tsakiya na Manchester City -- ya dauka na kamfe din yaki da masu kashe giwaye.

Masu kare gandun daji sun kiyasta cewa a shekarar 2011 kadai an kashe kimanin giwaye 17,000 ba bisa ka'ida ba.

An haramta cinikin hauren giwa a karkashin yarjejeniyar kasashen duniya.