Komfutar Dell na ' warin fitsarin mage'

Image caption Latitutde 6430u

Masu amfani da kamfutar Dell sun yi korafin cewar komfutar hannu ta Latitude 6430u na 'warin fitsarin mage'.

Injiniyoyin kamfanin Dell sun ce warin ba zai shafi lafiyar masu amfani da komfutar ba.

Yanzu haka dai masu irin komfutar sun maida wa kamfanin komfutocin don a sauya musu.

A watan Yuni ne, masu sayen kayan kamfanin Dell suka ce sabuwar komfutar na da wannan matsalar ta wari.

Wani mai amfani da kamfutar ya ce "a makwannin da suka wuce, na sayi sabuwar Latitude 6340u. Tana aiki da kyau amma tana warin fitsarin mage".

Karin bayani