Hollande ya tarbi Faransawa 4 a Paris

Faransa Nijar
Image caption Farasanwa da suka samu 'yanci

Shugaban kasar Faransa ya karbi 'yan kasar hudu da suka koma gida, bayan sakinsu da wasu 'yan bindiga da ake dangantawa da Al Qaeda suka yi garkuwa da su a hamadar Sahara.

Faransawan hudu da aka sake su ranar Talata a jamhuriyar Nijar sun isa Paris cikin wani jirgin sama mallakar gwamnatin Faransa.

An kama mutanen ne a ranar 16 ga Satumba 2010 a garin Arlit, inda su ke yiwa kamfanin Faransa, Areva, aikin hakar ma'adanin Uranium.

Kungiyar al-Qaeda a yankin arewacin Afrika ta ce mayakanta ne suka kama mutanen.

Ministan harkokin waje na Faransa Laurent Fabius ya ce ba'a biya fansa ba kafin a sako mutanen da yace suna cikin koshin lafiya.

Sai dai kuma kafafen yada labarai a Faransa na cewa sai da gwamnatin ta biya Euro miliyan 20 kafin a sako su.