Agaji ga 'yan gudun hijirar Najeriya

Najeriya
Image caption Dubban mutane ne ke kauracewa yankin arewa maso gabashin Najeriya saboda rikicin Boko Haram

Kwamishinan Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijira ya nemi Kasashen da ke makwabtaka da Najeriya da su bude kan iyakokin su ga 'yan Najeriyar da ke gujewa tayar da kayar bayan da kungiyar Boko Haram keyi a arewa maso gabashin kasar.

Wannan kiran dai ya zo ne bayan wasu mutane goma sha biyar sun mutu yayin da jami'an tsaron Kamaru ke kokarin mayar da su Najeriya da karfi da yaji.

Mai magana da yawun kwamishinan Kathryn Mahoney ta ce wadanda aka kashen su na daga cikin wasu 'yan Najeriya 111 da aka kama saboda shiga kasar ba tare da takardun izini ba.

Dubban mutane ne ke kauracewa yankin arewa maso gabashin Najeriya saboda rikicin Boko Haram.

Karin bayani